By Abbas Yakubu Yaura
Majalissar dokokin kasar Somaliya a ranar Asabar din data gabata ta amince da Hamza Abdi Barre a matsayin sabon firaminista, lamarin da ya share fagen kafa sabuwar gwamnati.
Dukkan ‘yan majalissun dokoki 220 da suka halarci taron sun san yawa Barre albarka, sannan aka rantsar da shi a ofis, in ji kakakin majalisar.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Kwankwaso Ba Shi Da Makoma A NNPP, Jam’iyyar APC Ta Nemi Ya Dawo Su Hade
Barre mai shekaru 48, ya shaidawa majalisar dokokin kasar cewa zai kafa gwamnati mai inganci da za ta mai da hankali kan “samar da kwanciyar hankali ta fuskar siyasa (wanda ya dace da) taken shugaban kasar Somaliya na sulhuntawa da duniya”.
Sabuwar gwamnatin Somaliya na fuskantar tarin kalubale da suka hada da matsalar karancin abinci da ke kunno kai da kuma masu tada kayar baya daga mayakan jihadi na Al-Shabaab.
A farkon wannan watan ne shugaba Hassan Sheikh Mohamud, wanda majalisar dokokin kasar ta zabe shi a watan Mayu, bayan an dauki tsawon lokaci ana gudanar da zabe mai cike da rudani da guguwa.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa sabuwar gwamnatin tana bukatar Ƙarfin tattalin arziki da ayyuka na yau da kullun domin samar da kyakkyawar rayuwa ga al’ummar Kasar da yaki ya dai dai ta.
“Gwamnatinmu tana da kyakkyawan shiri na siyasa wanda ke neman inganta tsaronmu, da karfafa tattalin arzikinmu da samar da ababen more rayuwa ga jama’armu,” in ji Mohamud a shafin sa na Twitter bayan an amince da Barre.
Akwai fatan fadar shugaban kasa ta Mohamud za ta ja layi a karkashin wani kazamin rikicin siyasa da ya durkusar da mulkin magabacinsa Mohamed Abdullahi Mohamed tare da yin barazanar sake jefa kasar cikin tashin hankali.
Shi kansa Mahmoud bai bayyana a zaman majalisar ba bayan da ya ce a ranar Juma’a ya kamu da cutar Covid-19.
Mohamud dai tsohon malami ne kuma mai fafutukar zaman lafiya wanda a baya ya taba zama shugaban kasa daga shekarar 2012 zuwa 2017 amma gwamnatinsa ta farko ta fuskanci ikirarin cin hanci da rashawa da rigingimu.