Yan majalisu sun amince da maida tara shigo da kayan fasa kwauri daga 1,000 zuwa 1,000,000
A ranar Laraba a ne, Yan majalisu suka sauya dokar shigo da haramtattun kayayyaki daga dubu daya zuwa miliyan daya.
Sun amince da tabbatar da dokar bayan Alkalai da hukumar Kare hakkin Dan adam sun gamsu da ita.
KARANTA:-Yan bindiga sun kashe Mutum biyu a Batsari, Kuma sun kada shanu 35
Michael Bamidele shine yace kodar ta dubu daya bazata hana masu shigowa da kayan fasa kwauri aikinsu ba.
A sashi na 35 na kudin, yace za’a ci tarar wanda aka kama miliyan uku, ko kuma shekara uku gidan kaso, idan Mutum yaki bayar da kayan za’a hada masa biyun.
A sashi na 39 na kundin, ya bada damar kwace kayan fasa kwaurin sannan a lalatasu, tare da sanya hukumomin da jami’ai ba Yan sanda kadai ba.
Yace wannan ya zama dole, saboda damar kwace kaya da lalatasu ba aikin hukuma daya bane kawai. Kamar yadda Bamidele yace.
Yace hakan zaiyuwu ne tare da aminciwar babban Ofishin Mai baiwa Jami’ai shawara.
Bamidele yace hakan yana da matukar amfani domin dukkan Jami’an suna karkashin kulawar gwamnati ne.