A zaman Yan majalisun Jahar Zamfara na jiya, sun gayyaci mataimakin gwamnanan Jahar Mahadi Aliyu tare da kwamishinan Ƴansandan na Jahar Husaini Rabi’u da su halarta a majalisa a ranar Talata 27 July, 2021. Kamar yadda Jaridar Channel Tv ta ruwaito
Zai gabata a gaban Yan majalisun ne bisa wani zanga-zangar da mataimakin gwamnan suka gudanar a garin Maradun cikin wannan hali na rashin tsaro dake addabar Jahar.
An yanke hukuncin gayyatar mataimakin gwamnan ne da kwamishinan Ƴansandan bisa kudirin da wani Dan majalisa mai wakiltar Maru Hon. Yusuf Hassan Kanoma ya gabatar.
KARANTA:- Buhari Zai Kaddamar da Layin Dogo daga Kano zuwa Kaduna
Yusuf Hassan Kanoma ya nuna rashin jindadinsa bisa kalaman da mataimakin gwamnan Jahar yayi a lokacin zanga-zangar, sannan duba da harin da Yan bindiga suka kai cikin awa ashirin da huda a garin Faru dake Karamar hukumar Maradun a Jahar Zamfara.
Hon. Yusuf Hassan Kanoma ya cigaba da cewa mataimakin gwamnan bai nuna rashin jindadinsa ba duba da kisan mutane sama da hamsin da akayi a harin da ya gabata, ya tara mutane don gudanar da zanga zangar duk da cewar kwamishinan Ƴansandan na dakatar dashi kan yin hakan.
Ya siffata irin wannan abun a matsayin rashin damuwa da kishin Al’ummarsa, yace mai irin wannan hali sam bai cancanta da kujerar mataimakin gwamnan ba.”
A wani labarin
Kotu ta yanke musu hukunci shekara uku gidan kaso bayan kulle Yarinyar su a firiza
Wata kotun Majistret dake Sokoto ta yanke ma Emmanuel Bassey tare da matar sa Esther Emmanual hukunci shekara uku gidan kaso, biyo bayan kulle Yarinyar su mai kimanin shekaru 12 a cikin firiza har na tsawon wata takwas
Mai shari’ar Shuaibu Ahmad ya kuma sanya musu tarar dubu ashirin da biyar kan wannan mummunan aikin da sukayi.
Sannan ya kara saka musu tarar dubu dari biyu da saba’in da biyar.
Yace an kama ma’auratan dumu dumu da laifin, ya kuma Kara musu zaman gidan kaso na wata sha biyu da kuma tara naira dari, tun da farko dai an yake musu hukunci shekara uku gidan kaso.
Mai shari’ar yace za su fara zaman gidan kasonne nan take.
Ya Kuma baiwa Goodness Emmanuel da Happiness Emmanuel yaran Emmanuel Bassey beli akan 500,000 ko wannen su.
Jaridar Tvcnews ta ruwaito a watan May, 2021, cewar an sanya wata yarinya mai kimanin shekaru sha biyu a cikin firiza.
A dai lokacin makotansu suka kai rohoto ga jami’an Yan sanda aka kubutar da Yarinyar, sannan aka kama wadanda suka aikata laifin.