An tabbatar da mutuwar ‘yan mata bakwai a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a jihar Jigawa a daren ranar Alhamis.
Majiyoyin yankin da suka zanta da BBC sun ce hatsarin ya faru ne a lokacin da kwale-kwalen ya ke kwaso matan daga Gasanya zuwa Gafasa.
Gafasa wani ganki ne da ke karamar hukumar Kafin Hausa, ya yin Gasanya ta ke a karamar hukumar Auyo, dukkan su a jihar Jigawa.
An ce wadanda abin ya shafa na dawowa ne daga halartar bikin Mauludi da aka yi a Gasanya.
Mikail Jibril, wanda ‘yarsa na cikin wadanda suka mutu, ya ce wadanda suka mutum sun kasance ‘yan tsakanin shekaru 10 zuwa 12 ne.
“Mutane 12 ne a cikin kwale-kwalen yayin da hatsarin ya afku a kogin da ke tsakanin kananan hukumomin Auyo da Kafin Hausa. Bakwai daga cikin ‘yan matan sun mutu yayin da aka ceto biyar,” inji shi.
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito Hakimin kauyen Gafasa, Adamu Abdullahi, yana cewa tuni aka binne wadanda suka mutu.