Kimanin ‘yan Najeriya 300 ne suka isa birnin Amman, babban birnin kasar Jordan lami lafiya domin gudanar da ziyarar kirista ta shekarar 2022 a kasa mai tsarki.
Maziyartan sun isa birnin Amman ne da sanyin safiyar ranar 17 ga watan Disamba domin gudanar da ibadar kiristoci ta kwanaki 9 a wuraren tarihi na koyarwar Yesu Almasihu kamar yadda aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki na Bible.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyyun PDP da APC Sun Mutu, NNPP Itace Mafi Inganci Da Sahihanci A Madadin – Kwankwaso
Gwamnan Enugu, Mista Ifeanyi Ugwuanyi ne ya dauki nauyin mahajjatan zuwa kasa mai tsarki.
A ranar farko ta ziyarar, Masu ziyarar sun gudanar da kewaye a wurin tarihi na Katadel wanda ke kan wani tudu a yankin Amman.
Citadel gida ne ga ragowa da abubuwan ban mamaki na wayewar da suka mamaye babban birnin Jordan.
A wurin, ma ziyaratan sun binciki ragowar Haikali na Hercules wanda Romawa suka gina da kuma gine-ginen da suka zama wani ɓangare na fadar Umayyad da kuma rugujewar cocin Byzantine na ƙarni na shida.
Daya daga cikin jagororin yawon bude ido, Mista Red’Ar, ya ce a lokacin Iron Age, Amman na yau ana kiransa “Rabbath-Ammon” kuma shi ne babban birnin mutanen Ammonawa na da.
Ar ya gaya wa ma ziyarrtan cewa Littafi Mai Tsarki ba shi da ranar karewa kuma alkawuran Allah ba su ƙarewa.
Ya kuma ja-goranci masu ziyarar don ganin gidan wasan kwaikwayo na Romawa mai ɗaukar mutane 5,000 inda Romawa suke taruwa don ba da hadayu ga Allah.
An kuma ba wa nasu ziyarar izinin shiga Gidan Tarihi na Archaeological na Jordan don ganin hotunan tarihi da kayan tarihi.
Ugwuanyi, kafin ya tashi daga birnin Enugu a ranar Juma’a, ya bukaci maziyartan da su kasance masu da’a a kasa mai tsarki, kada su tsere daga birnin Jordan.
Daya daga cikin maziyarartan, Mista Anselem Ekpungu, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na NAN cewa ziyarar ta ba shi damar ganin wurare da abubuwan da suka faru da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki.
Ya godewa Gwamna Ugwuanyi bisa wannan tallafin, inda ya yi addu’ar Allah ya kara masa lafiya yayin da yake ci gaba da daukar nauyin karin alhazai zuwa kasa mai tsarki.
A wani labarin kuma: Hotuna: Yadda Kwankwaso Ya Tarbi Tsohon Na Hannun Daman Ganduje
Tsohon dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muhyi Magaji Rimin Gado yammta tabbata yanzu ya zama ɗan jam’iyyar NNPP.
Wannan na zuwa ne bayan dakatar da shi da gwamnatin Kano tayi, daga shugabancin hukumar a kwanakin baya.