Tsohon Shugaban Kasar nan Goodluck Ebele Jonathan ya ce hakika yan Najeriya ba za su taɓa mance irin rawar da tsohon shugaban kasa Umar Musa Yar’adua ya taka a bangaren zaman lafiya da gina kasa ba.
Jonathan ya bayyana haka ne a wasu wallafe-wallafe da ya yi shafin sa na Tuwita yayin da ake alhinin cika shekara 11 da rasuwar Yar’adua.
Shugaban Yar’adua wanda ya karbi ragamar kasar nan a shekara ta 2007 ya rasu ne bayan fama da jinyace-jinyace a shekara ta 2010.
Gabannin rasuwar Yar’adua dai Jonathan shine Mataimakin shugaban kasa a wancan lokaci, kafin daga bisani aka naɗa shi a matsayin magajinsa a ranar shida ga watan Mayun 2010.
Ya ce “A yau ina cike da alhinin Dan gwagwarmaya, abokin aiki kana dan uwa a gare ni wato Shugaba Umaru Musa Yar’adua wanda Allah Ya Mishi rasuwa shekaru 11 da auka shudw”
“A matsayin mu na yan siyasa, mun kasnace muradin daya wato wanzar da zaman lafiya, hadin kai da kuma gaskiya da rikon amana. A kan haka shugaba Yar’adua ya doge har karshen rayuwar shi”
Daga bisani dai tsohon shugaba Jonathan ya bukaci yan Najeriya da su yi koyi sa kyakkyawan hali irin Yar’adua don gina kasar nan izuwa tudun na tsira.