Yan Najeriya basa danasani kan tsarin Kasarmu, Buhari ga Tsohon Firaminsta na Ethiopia
Juya akalar kasannan da tayi zuwa noma ya biyamu matuka, Kuma Yan Najeriya basa danasani akan haka, Inji Muhammadu Buhari.
KARANTA:-Harsashi ya kashe wata daga cikin masu zanga-zangar kafa kasar Yarbawa
Shugaban Kasa ya bayyana hakane lokacin da ya karbi bakuncin tsohon Firaminstan Ethiopia Hailemariam Dessalegn Boshe. a Abuja.
Yace ” dole ne mu komawa gona domin man Fetur ba zai daukemu ba, duba da yadda farahin yake sauka, a yanzu muna cin abunda muka noma ne, mun dakatar da shiwoga da kayan abinci sosai.
Yin noman kuma ya taimaka mana wajan samar da ayyukan yi, muna anfani da kayan zamani mutane da yawa sun bar Ofishin su sun koma gona, kuma basa danasani akan haka.
Tsohon Firaminstan ya yaba wa Buhari kan irin nasarori da gwamnatin sa ta samar, duk da matsalar cutar Covid-19.
Yace ya shigo kasar ne don kare hadin guiwar habbaka noma a Kasashen afirika, yace wannan kungiyar na aiki ne a kasashen afirika guda 16, Kuma idan muna son kawo sauyi dole mu fara da Najeriya.
Yace kasashen afirika dole suyi koyi da Kasar Najeriya, yanzu Najeriya ta cigaba kan hana shigo da shinkafa daga kasashen ketare. Dole muzama masu murya daya a Africa don zamu iya ciyar da duniya.