Fiye da ‘yan Najeriya 12,000 ne suka ci gajiyar shirin rage radadin talauci na shekarar 2022 na gidan agaji na Abu Bakr Al-Sidiq na Cibiyar Bayar da Agaji ta Sarki Salman dake Saudiyya.
Shirin ya kunshi raba kayan abinci ga mabukata musulmi da kiristoci a wasu jihohin kasar nan.
Shugaban kungiyar masu taimakon jama’a, Sheikh Abdul-Razaq Ibrahim Salman, a lokacin da yake jawabi a wajen kammala taron fara rabon a Ilorin, ya bayyana taron a matsayin babban nasara.
Ya ce rabon tallafin wani bangare ne na tallafin da Sarki Salman ke bayarwa duk shekara a fadin duniya wanda ya kunshi wadanda suka amfana a kasashe 19.
Ya godewa babban mai kula da shirin, Dr Abdullah Al-Rabeeha, da ya jagoranci shirin, ya kuma yaba da goyon bayan da ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ke ba wa shirin rabon kayayyakin.
Sama da tan 8,000 na abinci ne aka raba yayin da shirin yayin fara shirin, inda sama da mutane 4,000 suka amfana a Kwara, Kano, Abuja, da dai sauransu.
Nigeria dai na fama da tarin matalauta, wadanda abun da zasu sanya a bakin salati ma yake gagarar su.
Comments 1