A yammacin ranar asabar ne dai wani hoto mai cike da ta’ajibi ya karade shafukan sada zumunta na zamani.
Hoton wanda ya nuna Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje na taka hoton tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya dauki hankalin ma’abota shafukan na sada zumunta matuka, inda jama’a da dama suka yi ta tafka muharawa.
Shi dai Wannan hoto an dauke shi ne a yammacin ranar asabar jim kadan bayan kammala taron ranar Dimokuraɗiyya ta Najeriya tare da tarbar wasu da suka sauya sheka daga jam’iyyu daban-daban zuwa APC.
To sai dai galibin jama’a na nuna cewa halin da Ganduje ya nuna a hoton hali ne na taɓa, ko da yake an samu wasu kalilan da suka nuna farin cikinsu dangane da abinda ya yi, duk da cewa wasu na ganin hakan da siyasa.
A baya dai kamar yadda aka sani Kwankwaso da Ganduje sun kasance tamkar hanta da jini ne, da ake ganin rabuwar su za ta zamo da wahala, amma kwatsam cikin kankanin lokaci hidimar siyasa ta barranta su.
Toh ko ma dai Menene kawo yanzu da muke haɗa muku wannan rahoto, Sanata Kwankwaso bai ce uffan ba dangane da abinda tsohon yaron gidan nasa ya yi.