Hukumar karbar haraji ta kasa (FIRS) ta bayyana cewa ‘yan Najeriya zasu fara biyan haraji akan dukkanin wani rasiti da aka yi amfani da shi ta kafar sadarwa ta WhatsApp, ko kuma sakon kar ta kwana.
Hukumar ta ce za a dinga cirar haraji akan takadar ciran kudi ta na’urar POS da kuma mashin din cirar kudi na ATM.
Kamar yadda rahoto ya bagata, hukumar tace za a dinga biyan harajin ne a duk lokacin da aka cire wani rasiti.
Hukumar ta bada misali kamar haka; Akawun kamfanin ABZ ltd ya karbi kudi Naira dubu 500,000 daga Mista XYZ a madadin kamfanin ABZ ltd, kuma ya tura sakon cewa ya karbi kudi har dubu 500,000 daga Mista XYZ ta kafar sadarwa ta WhatsApp.
“Daga wannan misali, inda aka tabbatar da karbar dubu 500,000 dole ne a biya masa haraji”.