Gwamnan jihar Katsina kuma shugaban kungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma, Aminu Masari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai su yaki masu aikata laifuka da ke damun al’umma.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a Sokoto a ranar Alhamis a lokacin da ya jagoranci wata tawaga ciki har da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a ziyarar jaje da suka kai Sokoto kan harin da ‘yan bindiga suka kai a baya-bayan nan wanda ya yi sanadin mutuwar matafiya akalla ashirin da uku.
Ya ce ‘yan bindigar da ke ta’addancin kan ‘yan Nijeriya ba baki ba ne, mutane ne don haka ya kamata ‘yan Nijeriya su tashi su kare kansu daga ‘yan bindigaf.
Gwamna Masari ya yi tambaya kan dalilin da ya sa aka hana ‘yan Najeriya daukar makamai yayin da wadan da ake zargi da aikata laifuka a ko’ina suke rike da makamai.
Shi ma da yake jawabi, Gwamna Ganduje ya shawarci Gwamnatin tarayya da ta samar da na’urorin zamani wajen kwato dazuzzukan kasar tare da sanya ido kan ayyukan da ke gudana a fadin dazuzzukan kasar.
A nasa martanin Gwamna Aminu Tambuwal ya godewa gwamnonin bisa ziyarar da suka kawo.
Gwamnan jihar Sokoto ya bayar da shawarar a horas da matasan al’ummar da abin ya shafa tare da ba su makamai domin su zama runduna ta musamman domin kara kaimi ga jami’an tsaro na yau da kullum.
A cewarsa, hakan zai taimaka wajen dakile matsalar rashin tsaro a yankin.