Hukumar lura da lafiya ta duniya wato WHO a rahotonta na kwanan nan kamar yadda kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya labarto, ya nuna cewa akalla mutum dubu 800 ke kashe kansu a duk shekara a fadin duniya.
Rahoton WHO na 2016 ya nuna cewa akalla kashi 9.5 na wanda suka kashe kawukansu wanda ke dauke da adadin mutum dubu 100 ‘yan Nijeriya ne.
WHO ta ce tabbas wannan abin damuwa ne da fagaba na yadda mutane ke kashe kawukansu. Lamarin kashe kai laifi ne a dokokin Nijeriya, kamar yadda sashe na 327 na dokar Fenal Kod ya tabbatar, inda ya ce duk wanda aka kama ya yi yunkurin kashe kansa, akwai yiwuwar zai daure shi har na tsawon shekara daya a gidan yari.
Olayinka Atilola wanda yake Likitan masu fama da matsalar kwakwalwa ne, na Jami’ar jihar Legas, LASUTH, ya ce ba ya ga dalilan da wadanda suke kashe kansu suke bayyanawa, amma ya ce; ciwon hauka yana daga cikin abubuwan da ke sanya mutum ya kashe kansa. A cewarsa, mafi yawan wadanda suke kashe kawukansu, suna aikata hakan ne sakamakon cutar hauka. Ko kuncin rayuwa na yau da kullum.
Ya ce daga cikin abubuwan da ke sanya mutum kashe kansa sun hada da; damuwa, kunci, zaman kadaici, rashin fata, wanda wadannan dabi’u ke rayuwa a zukatan kowanne mutum a mataki-mataki.
Ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar ta bunkasa walwala da lafiyar al’umma a kowanne cibiyar lura da lafiya da ke fadin kasarnan. Sannan ya nemi da a rika tallagfawa wadanda suke yunkurin kashe kawukansu, inda ya ce hanya wacce ta fi wajen tallafawa masu yunkurin kashe kansu, shi ne ta hanyar; kai su wurin likitotin masu lura da lafiyar kwakwalwa.