Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC, ta gargadi al’ummar kasar kan yin taka-tsan-tsan tare da sanya idanu game da jabun alluran rigakafin korona da suka bazu a sassan kasar.
NAFDAC cikin gargadin da ta yi wanda ya janyo hankalin ‘yan Najeriyar ta ce jabun alluran rigakafin ka iya haddasa matsala ta Lafiya ga duk wanda ya yi kuskuren bayar da jikinsa don karbarsu.