A daidai lokacin da ake jimamin kisan manoman shinkafa fiye da 40 a garin Zabarmari dake karamar hukumar Jere a jihar Borno, ‘yan Nijeriya sun sabunta kiran da suke yi wa gwamnatin shugaba Buhari wajen ganin ya fatattaki shugabannin tsaron Nijeriya.
A ranar Asabar dai, Boko Haram suka yi wa manoma fiye da 40 kisan gilla ta hanyar yankan rago a wani kauye kusa da garin Maiduguri, lamarin da ya harzuka ‘yan Nijeriya a daidai lokacin da hotunan kisan manoman ya fita.
Bayanai sun nuni da cewa; ‘yan ta’addan Boko Haram din sai da suka daure manoman daga bisani suka yanka su.
Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum ne ya jagoranci yi wa manoman jana’iza.
Sai dai shugaban Buhari a daren jiya ya fitar da sanarwa ta hannun Kakakinsa, Malam Garba Shehu, inda ya ce shugaban kasar na Allah-wadai da wannan danyen aikin, inda ya bayyana kisan a matsayin ‘rashin hankali”. Inda ya tabbatar da cewa yana bai wa dukkanin hafsoshin tsaro goyon baya wajen ganin sun dauki matakan da suka dace wajen bai wa kasarnan kariya.
Sai dai hakan bai gamsar ba, inda ‘yan Nijeriya suka shiga shafukan sada zumunta suka caccaki kalaman na shugaban kasa Buhari, suna mai cewa haka aka saba a duk lokacin da aka yi wa ‘yan Nijeriya kisan mummuke, inda suka ce shugaban ya gaza wajen bai wa ‘yan kasa tsaro da kare rayukansu da dukiyoyinsu.
Suka kuma jaddada bukatar da yake akwai na korar dukkanin shugabannin tsaro da maye gurbinsu da kwararru tare da yi wa sashen tsaron garambawul da zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya.
Salihu Yakasai, wanda yake shi ne Kakakin gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce; abin takaici ne a ce ba wanda aka kora cikin shugabannin tsaron tun bayan aukuwar wannan lamarin.
Kakakin gwamnan, ya wallafa a shafinsa na Twitter @dawisu, cewa; “idan wannan bai sanya ka zubda hawaye ba, ban san mene ne zai sanya ka ba. Rayuka 43 suka farka suka fita neman abincinsu, amma suka tsinci kansu ana yanka su kamar tumakai. Bayan awa 24, ba wanda aka kora, ba wani kwakkwaran mataki da aka dauka, kuma nan da wasu awa 24 din, za a yi shiru, a kuma ci gaba da rayuwa”. Ya wallafa.
Haka zalika wani mai wasan barkwanci, Debo Adebayo wanda aka fi sani da Mr Macaroni, ya wallafa cewa; “ko dai ‘yan ta’adda su kashe mu, ko kuma jami’an tsaro su kashe mu. Ko ma yaya ne, kasarnan ana cikin tashin hankali. Ina gwamnati a lokacin da ake da bukatarsu? Ayya na manta. Suna nan suna zaluntar matasan Nijeriya”.
Shima fitaccen marubucin nan, Gimba Kakanda, ya caccaki shugaba Buhari bisa gazawarsa wajen yi wa ‘yan kasa jawabi kan wannan abin tashin hankalin.
“abin da ya kamata Buhari ya yi a yau shi ne ya bayyana gaban Talabijin, yana mai nuna takaicinsa da damuwarsa kan mutane da ya gaza bai wa kariya. Ya ayyana korar dukkanin shugabannin tsaro. Ko shugabannin soji na kasarmu ba su nuna halin ko in kula da kasar ba kamar yadda Buhari ke yi”.