Cutar Maleriya wacce ke kama al’ummar Nijeriya daga cizon sauro, a yau bayanai sun nuna cewa; cutar na addabar ‘yan kasar ne duba da yadda mafi yawan wadanda Jaridar Dimokuradiyya ta zanta da su, suka koka mata dangane da yadda cutar a yanzu ta zama ruwan dare gama duniya.
Salisu Abubakar daga garin Kaduna, daya ne daga cikin wanda wakilinmu ya zanta da shi a yayin da ya riske shi a bakin karamin asibiti ya je duba lafiyarsa, ya shaida cewa; ya kwashe kwana da kwanaki yana fama da zazzabi da ciwon kai, da kasala, da ya je aka gwada shi aka tabbatar masa da cewa; “Maleriya ce ta kama ni. Kuma akwai bukatar a yi min allurori har na kwana uku a jere. Sannan aka bani wadansu magunguna. Yau da ka ganni allura ta ukun na zo a yi min. Kuma Alhamdulillah na samu sauki.” In ji shi.
Sai dai ya ce; ya lura sakaci da ya yi da maganin sauro da kuma gidan sauro shi ne ya jaza masa har Maleriyar ta kama shi, “Amma duk da haka na fi tunanin cizon sauron yanzu kamar akwai annoba.” Ya tabbatar.
Ita ma Rahama Suleman, ta shaida mana cewa; lallai ita ma ta yi fama da zazzabi mai tsanani kwana biyu, zuwanta asibiti ne ya sanya har ta gane cewa Maleriya ne ya kamata. Sai dai ta ce; daidai gwargado gwamnati na iya bakin kokarinta wajen raba gidajen sauro, amma ta ce; sam ba ya isar kowa da kowa.
A karshe ta shawarci gwamnati da ta ci gaba da raba gidajen sauron kyauta. Sannan kuma ta bukaci a maishe da gidan sauron ya zama ba shi da tsada ko da kuwa za a rika siyar da shi. Sannan ta nemi al’ummar da suka amfana da karbar gidajen sauron su rika amfani da shi ta hanyar da ta dace.