IMG_20190902_204610

Yan Nijeriya Sun Yi Zanga-zanga A Ofishin Jakadancin Birtaniya

Gamayyar Kungiyoyin Fararen Hula ta gudanar da gangami a harabar ofishin jakadancin Birtaniya da ke birnin tarayya Abuja a Nijeriya domin nuna adawa da wani hukunci da wata kotun Birtaniya ta yanke kan Najeriya.


Kotun ta umurci gwamnatin Najeriya da ta biya wani kamfanin tsibirin Ireland, P&ID zunzurutun Dala biliyan 9.6 sakamakon karya ka’idojin yarjejeniyar kwangilar da ke tsakanin bangarorin biyu.


Gamayyar kungiyoyin ta bayyana hukuncin a matsayin damfara kan Najeriya, yayinda masu zanga-zangar dauke da alluna suka yi biris da ruwan saman da ake tafka wa a birnin na Abuja.


Wasu daga cikin allunan na cewa, “ Najeriya da Birtaniya aminan juna ne, ba makiya ba ne”. “ ‘Yan Najeriya miliyan 200 ba su amince da hukuncin Birtaniya ba.” “ Hukuncin Dala biliyan 9.6 damfara ce”.
Wasu alkaluman na cewa, “ Boris Johnson , ka taimaka wa shugaba Buhari wajen yaki da cin hanci.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *