Sama da ‘yan Nijeriya dubu 40 ne yaki ya tilasta musu tsallakawa zuwa Jamhuriyyar Nijar. Bbc Hausa sun labarto cewa; Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ‘yan gudun hijirar na tsallakawa ne daga arewa maso yammacin Nijeriya zuwa Nijar din sakamakon irin hare-haren da ake kai wa farar hula a yankin.
Ta bayyana cewa yadda ake kara samun tayar da zaune tsaye a jihohin Sakkwato da Zamfara da Katsina wadanda wasu kungiyoyi da ba Boko Haram ke kai hare-haren ba, sune suka haifar da mummunan yanayi a garuruwan da suke iyaka da Nijar.
‘Yan gudun hijira daga Nijeriya na ci gaba da kwarara zuwa kauyuka sama da 50 musamman a yankunan Guidan Roumji da Guidan Sori da Tibiri, a cewar hukumar.
Mai magana da yawun Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai Kula da ‘Yan Gudun Hijira wato Babar Baloch ya bayyana cewa ”sakamakon matsalar tsaro da ake samu a yankin Sokoto, muna dakon isowar wasu ‘yan gudun hijira zuwa Nijar.”
Babar Baloch wanda yake magana a wajen wani taron manema labarai a birnin Geneva na kasar Switzerland ya ce a Satumbar 2011 kawai, sama da mutane 2,500 ne suka yi kaura bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a Najeriyar.
Hukumar ta bayyana cewa tana aiki kafada da kafada da hukumomi a Nijar domin ba da agaji ga ‘yan gudun hijira wadanda wasunsu suna zuwa a zauce.
Hukumar ta bayyana cewa ‘yan gudun hijirar na ba da labarin cewa maharan na zuwa ne a shirye dauke da makamai.
Akasarin ‘yan gudun hijirar mata ne da kananan yara inda suke isowa dauke da alamu na tashin hankali a tattare da su, a cewarsa.
Wata ‘yar shekara 14 ta shaida wa hukumar cewa ‘yan bindigan da suka zo kauyensu sun kashe sama da mutane 50 harda ‘yan uwanta.
Ta bayyana cewa mahaifinta da kuma kannenta mata biyu ‘yan shekaru uku da hudu sun mutu nan take yayin da ‘yan bindigar suka bude musu wuta, inda kuma aka sari kaninta dan shekara biyar da adda.