Shugaban hukumar masu lura da masu bautar kasa wato NYSC reshen jihar Sakkwato, Philip Enaberue ya tabbatar da cewa; akwai wadansu mutum biyu mace da namiji da suke bautar kasa a Sakkwato da suka kaunaci juna har suka yi aure a tsakaninsu, wanda ya ce wannan shi ne karon farko da ya ga hakan a jihar.
An bayyyana Bello Abfulatif-Tobi da Fatima Hakeem a matsayin wadanda suka yi aure, inda ya ce; wadannan masu bautar kasar sun karbi shawarar shugaban NYSC na kasa hannu bibbiyu kuma suka dabbaka. Ya ce dukkansu ‘yan asalin jihar Osun da Oyo ne.
Ya ce an daura auren ne a yayin da dukkaninsu suke gudanar da ayyukansu a makarantar Sakandare ta gwamnati dake Tangaza. A cewarsa har Allah ya azurta ma’auratan da samun da mai suna Abdulkhalid. Inda ya shawarci sauran masu bautar kasa da su yi koyi da su.
Sannan har wala yau, Philip Enaberue ya tabbatar da cewa; biyu daga ciki masu bautar kasa guda 1,108 za su maimaita bautar kasa a jihar.
Enaberue, ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da manema labarai a Sakkwato, inda ya ce biyun da za su maimaita bautar kasa sun fito ne daga tawagar masu bautar kasa na shekarar 2018 Batch C Stream 1.
A ranar 3 ga watan Oktoba ne dai aka yaye su, inda aka mika wa sauran shaidar kammala NYSC din. Sannan ya kara da cewa; sannan akwai wani guda daya shima da aka kara masa watanni uku sakamakon fashin zuwa wurin aiki da ya rika yi.
Enaberue ya ci gaba da cewa; wadanda za su maimaita din an same su da laifin gujewa wurin aikin da aka tura su. Sannan ya tabbatar da cewa; za a karrama guda uku bisa nuna kwazonsu a yayin bautar kasar.
Comments 1