A yayin da yajin aikin da masu tuka Keke Napep da aka fi sani da ‘Adaidaita Sahu’ suka shiga a Kano ya shiga rana ta biyu, Masu aiki da Mababuran Haya wadanda akafi Sani da Okada da aka hana a birnin Kano kawo yanzu sun cika kan tituna suna gudanar da aiyukan su, yayin da jama’a ke neman Mafifa.
Yajin aikin dai ya kawo cikas ga ci-gaba a Kano a ranar Litinin din da ta gabata, lamarin da ya tilastawa jama’a da dama da suka hada da dalibai da ‘yan kasuwa zama a gidajensu saboda rashin motocin da za su kai su makarantunsu da wuraren aiki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yajin aikin na baya-bayan nan shi ne na biyu a cikin kasa da watanni 12 a birnin na Kano.
Matuka Keke Napep dai suna wannan yajin aikin ne ne don nuna rashin amincewarsu da kudin rajistar da hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano KAROTA ta Sanya musu.
Hukumar tana karbar Naira 18,000 a hannun sabbin masu rajista, yayin da ake sabuntawa masu shi akan Naira 8,000, a duk shekara.
Masu yajin aikin, wadanda suka yi fatali da hakan, sun ki fitowa aiki domin jigilar mazauna Birnin Wuraren aiyukansu a safiyar Litinin da kuma yau Talata.
Baya ga amfani da babura a matsayin madadin Keke Napep, a yanzu haka ana amfani da kananan motoci da masu zaman kansu wajen jigilar mutane daga Wuraren zuwa wani wurin, lamarin da ke kara jefa jama’a cikin fargaba kan matsalar rashin tsaro da garkuwa da mutane.
Da yake mayar da martani a ranar farko ta yajin aikin, Manajan Daraktan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano, KAROTA, Baffa Babba Danagundi, ya ce gwamnatin jihar za ta dauki tsauraran matakai don dakile yajin aikin.
Sai dai shugaban kungiyar Matuka Keke Napep na jihar Kano Sani Sa’idu Dankoli ya ce matakin bai zo da mamaki ba, domin an sanar da hakan makonni biyu da suka gabata.
Kazalika ya Kara da cewa, “Muna tattaunawa da mutanenmu don sake duba matakin saboda yawancin mu ba mu da abin da za mu ciyar da iyalansu sai dai idan Mun fita kullum. Muna ba ku tabbacin zuwa rana ta 2, za mu dawo.”