Rundunar Yan Sandar Najeriya dake Jihar Rivers ta Jibge dakarun ta sama da dubu goma sha bakwai a Jihar Rivers don bada tsaro a yayin zaɓen Kananan Hukumomi da zai gudana a Jihar.
Kakakin Rundunar a Jihar ta Rivers Nnamdi Omoni ya ce hakan ma dakarun yan sanda ba su kaɗai za su yi aikin ba, za kuma su samu tallafi daga sauran runduninin tsaro da za a jibge a Jihar.
A cewar shi, Kwamishinan yan sandar jihar Eboka Friday wanda kuma shine shugaban zauren tuntuba na rundunar tsaro dake kula harkokin zaben ya bada umarnin haramta wa duk wani hamshaqin mutum ko da dan siyasa ne zuwa rumfunar zabe tare da jami’an tsaron su.
Omoni ya ce jami’an yan sanda za su toshe dukkanin kafa ta shiga jihar daga daren ranar Juma’ar nan, har sai an ƙare zaben.
Ya kuma bukaci jama’ar gari da su bada hadin kai wa jami’an yan sandar da aka tura don bada tsaron, wanfa hakan zai yi silar gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.
A bangaren gwamnan Jihar Mista Nyesom Wike ya bada tabbacin cewa za a gudanar da zabe na gaskiya da gaskiya ba tare da nuna wani bangaranci ba, don haka ya bukace su da su guji duk wata aika-aika yayin zaben.
Daga bisani dai ya bukaci jagororin jam’iyyu sha bakwai da za su baje baiwar su a yayin zaben da su kwaɓi mabiyan su kan su zamo masu bin doka da oda.
A gobe Asabar ne dai al’ummar jihar ta Rivers za ta fita kwai da Ƙwarƙwata a faɗin kananan hukumomi 23 na Jihar don kada kuri’a.