• Rundunar Yan sanda ta Katsina ta kashe wani Dan bindiga, Kuma ta kubutar da wata Tsohuwar.
• Jami’in hulda da jama’a na rundunar jihar Gambo Isa ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis.
• Ya ce Dan bindigan ya yi kokarin tserewar ne tare da matar da yayi garkuwa da ita hakan yasa jami’an yan sanda suka bude mashin wuta.
Jami’an rundunar Yan sanda ta kasa reshen jihar Katsina, sun yi nasarar kashe wani Jigo na yan bindiga mai suna Abdullahi Ummi, a wani bata kashi da suka yi da dan bindigan.
Jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Gambo Isa ne, ya bayyana hakan, a zantawar shi da manema labarai a jiya Alhamis, a garin Katsina.
Gambo ya ce, Dan bindigan ya boye ne a wani yanki da ake cewa Gullu, dake cikin wani daji na karamar hukumar Yankwashi dake jihar Jigawa.
Ya kara da cewa, Dan bindigan na da kimanin shekara Hamsin ne, Kuma ya yi garkuwa da wata dattijuwar mai shekara 80 mai suna Hassan Zubairu, dake karamar hukumar Sandamu na jihar Katsina, inda ya bukaci ya’yan ta da su ba shi, Naira milliyan dari biyar a matsayin kudin fansar mahaifiyar su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kashe wani babban jami’in soji a hanyar Abuja zuwa Lokoja
“Bisa samun wasu ingantattun bayanan sirri, jami’an mu suka afka maboyar Dan bindigan dake cikin dajin, domin farmakan shi” inji shi.
” Lokacin da ya yi yunkurin gudu a kan mashin din shi, tare da dattijuwar da ya yi garkuwa da ita, sai jami’an mu suka bude wa Dan bindigan wuta, inda a nane su kayi nasarar kashe shi” inji jami’in Hulda da jama’an.
A cewar jami’in Hulda da jama’an, an yi garkuwa da matar ce, a ranar 29 ga watan Yunin shekarar nan, Kuma Jami’an yan sanda jihar ta Katsina, sun yi nasarar ceto tane, a jiya Alhamis 15 ga watan shekarar 2021.
Comments 1