Hukumar tsaro ta ‘yan sandan Nijeriya a Sakkwato, sun shawarci Malamai akan su kaucewa gabatar da jawaban tunzura jama’a musamman a daidai wannan lokaci na annobar korona da kuma za a gudanar da bukukuwan sallah.
Har wala yau ‘yan sandan sun shawarci al’umma da su kasance masu bin ka’idojin dakile yaduwar annobar cutar korona a yayin bukukuwan sallah.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Kaoje ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da Kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Muhammad Sadiq a ranar Laraba.
Kaoje ya tabbatar da cewar hukumar a shirye take wajen samar da tsaro tare da kare rayuka da dukiyar al’umma a kowanne lokaci. A don haka ya tabbatar da cewa; jami’an ‘yan sandan jihar na kowanne sashe an raba su a fadin garin Sakkwato domin tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar baki daya.
Har wala yau rundunar ‘yan sandan sun shawarci Malaman addinin Musulunci da su kaucewa jawaban da ka iya tunzura jama’a, inda suka ce masallatai ba wurin yiwa wasu kamfen bane musamman ma a lokacin annobar korona din nan.
“Ba a amince da bangar siyasa ba, ko gabatar da jawaban siyasa a wuraren ibadu ba.” Inji rundunar.
‘Yan sandan sun kuma shawarci bata gari da sauran ‘yan ta’adda su yi maza su bar jihar, domin tuni rundunar ta baza jami’anta domin tabbatar da tsaro a jihar.