Rundunar Yan Sandar Jihar Zamfara ta yi nasarar kubutar da wasu mata hudu da aka yi garkuwa da su a kauyen Bilbis dake karamar hukumar Tsafe na jihar.
An samu nasarar ceto matan ne da aka yi garkuwa da su makonni uku da suka gabata bayan binciken sirri tare da matsin lamba da jami’an Maido da zaman lafiya na Operation Restore Peace suka yi a jihar.
Da ma dai Kwamishinan yan sandar jihar CP Hussaini Rabiu ne ya bada umarnin jibge jami’an tare da fatan maido da matan.
Yanzu haka dai tuni aka bada kulawar lafiya ga matan, inda kuma a yanzu haka rundunar ta ce tana kan aiki tukuru don zakulo wadannan yan bindiga dake da hannu dumu-dumu a aika-aikar.