By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan Najeriya har yanzu bata samar da isassun motocin sintiri da na’urorin rediyo na sadarwa ba ga akasarin ma’aikatantan ‘yan sanda duk da cewa ta karbi kudi Naira biliyan 58.9 na manyan ayyuka a cikin shekaru shida da suka gabata.
Binciken kasafin kudin ‘yan sanda daga shekarar 2015 zuwa 2020 ya nuna cewa rundunar ta gabatar da Naira biliyan 115.8 na manyan ayyuka yayin da gwamnatin tarayya ta saki kimanin kudi Naira biliyan 58.9 ga hukumar.
Abubuwan dake cikin kasafin kudin sun hada da Samar da kayayyakin tsaro,na’urorin zirga-zirgar jiragen sama, kananan motoci da manyan motoci, na’urorin masana’antu, litattafai, ofisoshin ‘yan sanda,da barikin ‘yan Sanda, gyara gine-ginen gidaje da ofisoshin ‘yan sanda, jiragen sama, da kayan aikin kiwon lafiya.
A shekarar 2020, babban kasafin kudi ya kasance na naira biliyan 14.2 amma adadin da aka fitar ya kai Naira biliyan 12. A shekarar 2019, ‘yan sanda sun samu biliyan 6.3 daga cikin kudi Naira biliyan 22,064,903 yayin da Naira biliyan 11.9 wanda aka fitar daga cikin Naira biliyan 25.1 wanda aka ware a kasafin kudi na shekarar 2018.
A shekarar 2017, an ce an fitar da Naira 9,099,136,000 daga cikin Naira biliyan 20.1 da aka tsara na manyan ayyuka ga hukumar yayin da aka fitar da Naira 10,026,818,000 daga cikin mayan ayyukan kasar na Naira biliyan 16.1 a shekarar 2016.Hukumar ta NPF ta samu kudi kimanin naira biliyan 8.9 daga cikin Naira biliyan 17.8 data gabatar a kasafin kudin ta na shekarar 2015.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Duk da cewa ma’aikatar harkokin ‘yan sanda ta ware kudi kimanin Naira miliyan 20 don samar da na’urorin sadarwa na radiyo ga hanyoyin tsaro ga ‘yan sanda a cikin kasafin kudinta na shekarar 2020, babu wata shaida da ke nuna cewa an kawo na’ororin kayan aikin.
Bincike ya nuna cewa hukumar ‘yan sanda da tsare-tsare na da kasafin kudi na Naira biliyan 2,037,820,626, 202 daga cikin Naira biliyan 7,786,923,450,732 da gwamnati ta ware domin tsaron kasa tsakanin shekarar 2015 zuwa 2020.
Jami’an ‘yan sandan da suka nemi a sakaya sunansu saboda tsoron takunkumin, sun ce manyan jami’ai ne kawai ake baiwa na’urorin sadarwar radiyo,inda ya kara da cewa ‘yan sandan dake sintiri sun dogara da wayoyinsu na hannu don yin magana da manyansu idan bukatar hakan tata so.
Kakakin ma’aikatar harkokin ‘yan sanda Bolaji Kareem, ya bayyana cewa motocin da aka tanadar wa ‘yan sandan na dauke da na’urorin sadarwa.Da aka tambaye shi game da adadin na’urorin sadarwa na radiyo nawa aka baiwa ‘yan sanda da naira miliyan 20 a cikin kasafin kudin ma’aikatar, sai ya roki a ba shi lokaci domin ya gano hakan.
Kwamishinan ‘yan sandan dake wakiltar kafafen yada labarai a hukumar ‘yan sanda, Austin Braimoh, ya koka kan yadda ake ware motocin ‘yan sanda da dama ga gidajen ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati, ya kara da cewa ‘yan Najeriya su kara damuwa da jin dadin ‘yan sanda.
Comments 1