Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen jihar Edo sun kashe wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a yayin wani artabu da ‘yan sanda a jihar Edo.
Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a dajin Ughiole da ke karamar hukumar Etsako ta Yamma a jihar a ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Dage Shari’ar Gwamnatin Tarayya Da ASUU
Majiyar Dimokuradiyya ta samu labarin cewa ‘yan sanda na aikin kota kwana a wani wurin da ke da bututun mai, sai wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka zo wurin
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Chidi Nwanbuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, “A ranar 11 ga Satumba, jami’an da DPO na Agbede ya jagoranta yayin da suke aikin kula da bututun mai na dajin Ughiole a karamar hukumar Etsako ta Yamma, kwatsam sai suka ci karo da wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka fito daga dajin. ”
Ya ce ‘yan bindigar da suka ga ‘yan sandan suka bude musu wuta, ana cikin haka ne aka kashe daya daga cikinsu a lokacin da yake kokarin tserewa cikin dajin.
SP Nwanbuzor ya ce wasu da ake zargin sun tsere zuwa cikin dajin da raunuka daban-daban a yayin da ake ci gaba da shuga dajin domin kamo ‘yan kungiyar da suka tsere.
Kakakin runumdunar ya bayyana cewa an kwato bindiga guda daya na gida, layu, da kudi Naira 240,000.00 daga hannun wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne.
A WANI LABARIN KUMA: 2023: Za Mu Aike Da Atiku Gidan Ritayarsa A Dubai, Inji Shettima
Sanata Kashim Shettima, dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya bayyana Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, a matsayin da siyasar yawon bude ido da ke barin kasar nan zuwa Dubai, hadaddiyar daular larabawa don yawon shakatawa.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Tsohon gwamnan jihar Borno ya ce idan har kyakkyawan tarihin bayar da hidima, jagoranci nagari da kuma iya daukar ƙwararrun masu gudanar da mulki sun kasance ma’auni, Atiku ba zai iya daidaita kansa da Asiwaju Bola Tinubu, ɗan takarar APC ba.