Daga: Abbas Yakubu Yaura
Jami’an ‘yan sandan da ke aiki a sashen Iju,a jihar Legas sun cafke wasu jami’an sojojin bogi hudu.
An kama sojojin na jabu ne a wata mota kirar Mazda ranar Lahadi 24 ga watan Yuli da misalin karfe 1:30 na rana a unguwar Iju da ke Legas.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/yan-taaddan-da-ke-barazanar-shirin-sace-buhari-el-rufai-zasu-kawowa-yan-najeriya-sauki-ne-omokri/
Wadanda ake zargin sun hada da Samuel Abel mai shekaru ‘28, Victor ljeemai 35, Lukman Salabiu 43 da Oyinyechi Macus mai shekaru 30.
A cafke sune yayin wani sintiri na yau da kullun karkashin jagorancin CSP Gbenga Stephen, jami’in ‘yan sanda na sashen Iju.
Da yake tabbatar da kamun, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce an mika wadanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na Yaba dake jihar domin ci gaba da bincike.”
Idan zaku iya tunawa Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa makonni biyu da suka gabata jami’an ‘yan sandan da ke aiki da sashin Orile sun kama wani sojan bogi a hanyar Sari-iganmu, Orile.
A Wani Labarin Kuma Manajan Daraktan Kamfanin Mai Na Fatakwal Ahmed Dikko ya bada tabbacin cewa za’a kammala aikin gyaran tsohuwar matatar man fetur ta Port Harcourt mai karfin tace ganga 60,000 a kowace rana. kuma za’a yi amfani da shi a kashi na farko na shekarar 2023.
Dikko ya bayar da wannan tabbacin ne a ƙarshen mako a lokacin da kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai kan harkokin matatun man kasar, da ya ziyarci matatun man da ke jihar Ribas domin tantancewa a nan take.
Ya ce tsohuwar matatar mai ta Port Harcourt da ake kira ‘Area 5’, za ta fara aiki a farkon kashi uku na aikin.
Ya ce a lokacin da aka kammala aikin gaba ɗaya a ƙarshen shekarar 2024, ginin zai samu ƙarfin tace kayan aikin da ya kai 210,000 bpd.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa za su tsaya kan ka’idojin da aka tsara da kuma cikin kudin da aka amince da su na aikin.
Ya ce, “Mun shirya kammala Area 5 nan da kashi na farko na shekara mai zuwa, domin mu fara gudanar da shi.
Ita ce tsohuwar matatar mai. Ita ce injin sarrafa ganga 60,000 a kowace rana kuma ita ce fifiko a gare mu a wannan lokacin. “Sauran sassan matatar man za su zo bayan ƴan watanni.
Muna kan hanya da sarrafa tsarin da kyau kuma za mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu a kowane lokaci don tabbatar da cewa mun cika waɗannan tsammanin da muka sa kan kanmu don haka dukkanmu za mu yi alfahari da duk waɗannan ayyukan kuma mu fara samun damar tacewa a Fatakwal.”
Ya nuna godiya ga majalisar wakilai bisa goyon bayan da suka bayar.
Shugaban Kwamitin Wucin gadi na Majalisar, Honarabul Ganiyu Johnson, wanda MD ya jagoranta tare da mambobinsa sun nuna gamsuwa da matakin aiki.
Ya ce, “Ya zuwa yanzu a madadin ‘yan kwamitina, mun gamsu da matakin aikin, domin ba mu yi tsammanin irin wannan aikin ba lokacin da muka bar Abuja. Amma bayan zagaye, mun gamsu da matakin aiki.
“Ya kamata ‘yan Najeriya su hakura da kamfanin. Mun san cewa mafita ce ga duk tallafin mai ita ce matatun mai. Tallafin mai zai zama tarihi. Ya kamata mu iya rage shi zuwa mafi ƙanƙanta.
“Muna bin ‘yan Najeriya hakkin mu tabbatar da cewa wannan wurin yana aiki domin idan wadannan matatun man ba sa aiki, za mu ci gaba da shan wahala kuma Allah Ya kiyaye, muna fatan ba za a kai ga matakin da talaka ba zai iya siyan man fetur ba, shi ya sa a gaske muke. ina son karfafa muku gwiwa da tallafa muku da kuma tabbatar da kun kammala wannan matatar. Ko da a Port Harcourt ne kawai, hakan na nufin za mu iya isar da bpd 210,000.”
Ya bukaci MD da ya gaggauta bin diddigin kammala aikin matatar tare da tabbatar da an kai shi a kan kari