Jami’an ‘yan sanda a Kaduna sun cafke mutum biyu da ake zarginsu da garkuwa da jama’a da kuma wani da ake zarginsa da siyar da makamai a jihar.
ASP Mohammed Jalige, jami’in hulda da jama’a PPRO, shi ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya fitar a ranar 20 ga watan Janairun nan, inda ya ce rundunar Operation Yaki ce da suka fita samame a titin Gamagira zuwa Soba Road, dake karamar hukumar Soba LGA suka kama wani babur da ba shi da lamba, inda suka kama mutum biyun din masu suna Musa Sabiu mai shekara 40 da Umar Sule mai shekara 30 wanda suka fito daga kauyen Tampol dake karamar hukumar Kachia a jihar.
Ya ce bayan ‘yan sandan sun binciki babur din su an samu harsasai guda shida da kuma adda da wayoyi guda biyu da kudi har naira dubu hamsin.
Ya ce da zarar sun kammala bincikensu za su mika su ga kotu.