Daga: Abbas Yakubu Yaura
Jami’an rundunar Sufeto-Janar na ‘yan sanda IGP da na IRT sun kama wasu masu ba da labari ga wata kungiyar masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, wadda ta yi garkuwa da matar aure da ’ya’yan wani dan majalisa, Hon.Dr Ibrahim Aminu, a jihar Katsina.
IRT ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakatariyar ta fitar a ranar Lahadi, 28 ga watan Agusta, 2022.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yajin Aiki Ya Shiga Kwanaki Na 196, Yau Ne ASUU Zata Yanke Shawara
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bakori a majalisar dokokin jihar Katsina a watan Satumbar shekarar 2021 inda suka yi awon gaba da iyalansa.
Manyan wadanda ake zargin, Muttaka Ibrahim, Suleiman Rabiu da Surajo, maza ne kuma ‘yan asalin karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina, an kama su ne bisa zarginsu da bayar da bayanan da suka kai ga farmakin da aka kaiwa dan majalisar tare da yin garkuwa da ‘yan uwansa.
A ci gaba da rahoton da hukumar leken asirin ta yi kan ayyukan ‘yan ta’addan masu kisan kiyashi da jami’an IRT da ke aiki da rundunar ‘Operation Restore Hope’ na rundunar ‘Operation Restore Hope’ a kauyen Yankwani da kuma garin Kurani ke aikatawa, rundunar ta kai dauki tare da cafke wadanda ake zargin a maboyarsu daban-daban.
Yayin gudanar da bincike, Muttaka Ibrahim ya amsa laifin da ya aikata inda ya ce shi da wasu ’yan kungiyar masu bada labari ne ga Sanni Tukur AKA Abacha suna ta’addancin ga al’ummar kauyuka da garuruwa a jihohin Katsina da Zamfara.
An ce sun bayar da bayanan sa kai ne ga shugaban ‘yan bindigar da ya kai ga yin garkuwa da matar Hon.Dr. Ibrahim Aminu da wasu shida ‘yan kasar.
Sauran wadanda kungiyar ta’addancin ta shafa sun hada da Buhari Usman, wanda aka fi sani da Fedeco, Nazaradeen Ibrahim, Amandallah Ahmad, Ibrahim Suleiman, Sumayya Nura da Yahaya Bura wadanda a halin yanzu suke hannun kungiyar.
Masu garkuwa da mutanen bayan sun yi garkuwa da matar dan majalisa Rabi Yusuf da ’ya’yansa maza biyu dukkansu ‘yan karamar hukumar Bakori sun bukaci a basu naira miliyan goma sha daya da naira miliyan goma ga ‘ya’yansa a lokuta daban-daban.
Da ake yi masa tambayoyi, dan fashin, Muttaka Ibrahim, ya amsa cewa an biya shi Naira dubu dari da talatin (N130,000) daga hannun shugaban kungiyar ya kara da cewa wani Yusuf Bala na Zariya ne abokinsa.
Ya kuma yarda cewa shugaban ‘yan fashin ya karbi jimillar naira miliyan shida da dubu dari biyar daga dangin wadanda suka yi garkuwa da su a garin Yankwani.
Da yake bayyana halin da ya shiga, dan majalisar ya shaida wa masu binciken ‘yan sanda cewa ya biya jimillar kudi har naira miliyan talatin da bakwai da dubu dari biyar ga shugaban kungiyar domin a sako dan uwan sa daga hannun ‘yan fashin.
Har yanzu dai ‘yan sandan na ci gaba da bincike duk wadanda ake zargin kuma za a gurfanar da su a gaban kotu idan aka same su da laifin a cewar shugaban tawagar.
Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, ya bayar da umarnin a bi duk makamai, da alburusai da ke hannun ‘yan ta’addan ta hanyar duk wani kokari.
Hukumar ‘yan sandan ta bakin Kakakin Rundunar, CSP Muyiwa Adejobi ta bayar da tabbacin cewa za a gurfanar da duk wadanda ake tuhuma a gaban kuliya kamar yadda dokar kasa ta tanada.
A wani labarin kuma Mutane 30,000 Ne Suka Mutu Sakamakon Gurbacewar Iska A Jihar Legas – LASEPA
Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Legas ta bayyana cewa gurbacewar iska ce ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 30,000 a Legas a shekarar 2021.
An bayyana hakan ne a wata takarda da hukumar ta rabawa manema labarai wanda jaridar PUNCH ta samu a ranar Lahadi.