By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta cafke wani mutum mai suna Ismaila Wasiu da Mutairu Shittu da laifin kashe wata mata mai suna Mujidat a unguwar Ayekale Saki a jihar Oyo kuma suna hannun.
Jaridar Dimokuradiyya ta samu labarin cewa wanda ake zargin abin ya rutsa da shi ne daga jihar Legas ta hanyar yin kiran waya da daya daga cikin wadanda ake zargin.
Da yake tabbatar da rahoton, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso, ya ce an ajiye gawar da aka kashe a dakin ajiyar gawa, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin.
Rundunar ‘yan sandan ta bukaci mazauna yankin da su tallafawa hukumar wajen yaki da miyagun laifuka ta hanyar ba da bayanan sirri.