By Abbas Yakubu Yaura
A cikin wata Sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta fitar tace mutane 242 daga cikin wadanda aka kama suna fuskantar shari’a a gaban kotuna daban-daban na jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige ne ya fitar da sanarwar a ranar Laraba a Kaduna.
Jalige yace rundunar ta ci gaba da jajircewa wajen ganin ta kawar da barayi, ‘yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.
“Hakan ya kai ga kama mutane 305 da ake zargi da hannu a hare-haren ‘yan bindiga da fashi da makami da garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja da sauran kananan hukumomin jihar Kaduna.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A cewarsa, rundunar ta samu nasarar kwato manyan bindigogi da makamai guda 161, da alburusai 2,924 a cikin wa’adin da aka sanya wa hannu.
Jalige ya kuma ce an samu nasarar ceto mutane 168 da aka yi garkuwa dasu tare da sake haduwa da iyalansu.
“Rundunar dake karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda CP Madussiru Abdullahi, zata ci gaba da mai da hankali wajen sauke wadannan ayyukan da suka rataya a wuyansu.
“Rundunar ta kuma umurci duk masu ruwa da tsaki a yakin da ake yi da rashin tsaro dasu daina yin kalaman da zasu iya kawo cikas ga yakin da ake da ‘yan fashi da sauran laifuffuka, ba a jihar Kaduna kadai ba, har ma da kasa baki daya.
Kazalika Kwamishinan ‘yan sandan yace wadannan kalamai ba za su sa ‘yan sandan su karaya ba ta kowace hanya, ya kuma yi alkawarin kamawa tare da gurfanar da bata gari dake da niyyar kawo cikas ga tsarin zaman lafiya a jihar”.
Sannan ya bukaci mazauna jihar dasu gaggauta kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da yankinsu a duk lokacin da suka ga bakuwar fuskar da basu yarda da ita ba.