Dakarun ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Borno sun samu nasaran kama wani rikakken mayaki a kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram mai suna Aliyu Ibrahim
Aliyu Ibrahim kwararren mayaki ne a harkan ta’addanci, ya halarci yakukuwa na kungiyoyin ta’addanci a Nigeria da kasashen waje, ya halarci manyan hare-haren ta’addanci da kungiyar Boko Haram ta kaddamar a kasashen Kamaru, Chadi da Nijer
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Borno CP Muhammad Aliyu shi ya bayyana wannan labarin, kuma an kama kwararren ‘dan ta’addan wato Aliyu Ibrahim tare da yaransa guda uku a garin Kikwa dake jihar Borno
Allah Ka taimaki rundinar ‘yan sandan Kasarmu Nijerya akan ayyukan ta’addanci, Allah Ka basu nasara Amin