Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta damke wani malamin makaranta mai zaman kansa da laifin yin lalata da wasu yara mata guda biyar a ajinsa wadanda ya sha jawo su cikin bandaki domin yin lalata dasu.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah wanda ya gabatar da wanda ake zargin mai shekaru 25, Umar Isah a hedikwatar jihar a ranar Juma’a, binciken da suka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya aikata hakan ga wasu yaran da ke daukar darasi a ajin sa.
KARANTA WANNAN LABARIN:N150,000 na ke samu kullum da sana’ar wankin mota, Dirarriyar budurwa
Wanda ake zargin wanda ya amince da aikata laifin yayin da yake bayar da bayanin nasa na ikirarin ya ce: “A cikin ajin kamar falo ne mai karamin daki. Don haka sai na shigar da su cikin dan karamin daki daya bayan daya, in cire hijabinsu in yin lalata dasu”.
Lokacin da aka tambaye shi ko yana cikin sihiri don yin hakan, wanda ake zargin ya ce: “A’a. Ba wani boka ko Mallami da ya umurce ni da yin haka ba. Kawai dai na tsinci kaina ina yin hakan.”
Rahoton ‘yan sandan ya kara da cewa: “A ranar 10/11/2022 da misalin karfe 10:00 na safe, wadannan mutane da suka hada da Hussaina Rabe, Basira Umar, Khalid Ibrahim da Zainab Ibrahim dukkansu mazauna kauyen Shargalle, karamar hukumar Dutsi ta jihar Katsina, sun kawo rahoton hadin gwiwa a sashin Dutsi na jihar Katsina.
Inda suka bayyana cewa akwai wani Umar Isah, ‘M’ mai shekaru 25 a karamar hukumar Mashi, malamin ajinsu, ya ce a lokuta daban-daban, wanda ake zargin ya yi amfani da ‘ya’yansu mata wanda (aka sakaye sunansu) ya shigar da su bandakin makarantar ya sa yatsa a cikin al’aurarsu.
A yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa aikata laifin, Ana ci gaba da bincike.”
A wani labarin kuma, Tinubu Ba zai Halarci Taron Tattaunawa da Yan Takarar Shugaban Kasa Ba
A Wani Labarin Kuma, Shekaru 11 na kwashe ina soyayya da yayana, shi ya raba ni da budurcina, Budurwa
Na shafe shekaru 11 ina soyayya da dan’uwana na jini, wanda takai ga ya kawar mun da budurcina
Hakan ya fara ne lokacin da iyayenmu suka yi tafiya zuwa Amurka na wasu watanni kuma aka bar ni da babban yayana a gida guda.gospelarea.com ta rawaito.
Watarana ina wanka sai na manta towel dina sai na nemi yayana ya taimakeni da tawul din sai ya ganni tsirara sai ya yi mamakin lankwasa na ya fara yabona, bai dade ba ya yi sauri ya fara sunbatata kuma a ranar mun sadu da juna sai ya karya mun budurcina!N.