By Abbas Yakubu Yaura
‘Yan sanda sun kama tare da gudanar da bincike a kan wasu ‘yan uwa biyu, Chima Nnamani da Michael Nnamani, bisa zarginsu da hannu wajen yi wa wata karamar yarinya ‘yar shekara tara fyade a yankin Enugu.’Yan’uwan biyu, wadanda iyayensu daya ne, sun fito ne kuma suna zaune ne a cikin al’ummar Akpawfu dake karamar Hukumar Nkanu ta Gabas ta Jihar Enugu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, ASP Daniel Ndukwe, ya tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a garin Enugu ranar Asabar.
“Bayan karar wadanda ake zargi da hannu a cikin zargin yin lalata da wata yarinya yar shekara tara duk an mika su zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar (CID), Enugu, domin gudanar da cikakken bincike,” inji shi.
Shugabar kungiyar mata ta (WACOL), Farfesa Joy Ezeilo, ta yi kira da a gaggauta gurfanar da mutane biyun wadanda ake zargin da laifin yin lalata da karamar yarinyar a cikin wata al’umma a jihar Enugu.
Ezeilo, wanda kuma shi ne Babban Darakta na WACOL, ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Enugu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sanarwar ta kara da cewa: “A ranar 28 ga watan Nuwamba, 2021, WACOL ta samu karar yin lalata da wata karamar yarinya ‘yar shekara tara da wasu ‘yan uwa biyu wadanda iyayensu daya ne, Chima Nnamani da Michael Nnamani, daga yankin Akpawfu suka yi.
“An kama wadanda ake zargin ne da laifin cin zarafin wata ‘yar uwarsu yar shekara tara da ke zaune tare da su.
“Yayin data ke bayar da labarin irin halin data shiga a hannun wadannan masu aikata laifin, wadda abin ya shafa ta bayyana yadda wannan danyen aikin da aka yi mata da cewa ya fara ne nan take a lokacin data isa wurin da suke zauna tare dasu a matsuguninsu kuma ta ci gaba da zama a kullum musamman da safe.
“Bayan rahoton, WACOL ta kai karar su wajen ‘yan sandan Najeriya (MTD), Garki, Awkunanaw a Enugu, lamarin daya kai ga kama Michael Nnamani da dan uwansa, Chima Nnamani, wanda dalibi ne a Jami’ar Uyo.
“Don haka WACOL ta bukaci ‘yan sandan Najeriya dasu gaggauta daukar mataki kan lamarin ta hanyar gurfanar da karar a gaban kotu kamar yadda dokar laifuka ta jihar Enugu da kuma dokar hana cin zarafin jama’a (VAPPL 2015) ta jihar Enugu.” Tayi.