Rundunar yan sandar Jihar Imo ta tabbatar da labarin kisar tsohon mai baiqa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin Ahmad Gulak.
To sai dai wata sanarwa mai kama da almara da hukumar ta fitar jim kadan bayan hallaka ɗan gidan siyasar ta APC, ta ce ya bar hotel ne ba tare da saninsu ba.
Sanarwar ta ce lallai rundunar yan sanda ta samu labarin cewa wasu yan bindiga da kawo yanzu ba a kai ga tantance ko su wanene ba, sun yi kwantan bauna wa Gulak da wasu karin mutane biyu, yayin da suke hanyar su ta zuwa Filin Jirgin Sama na Sam Mbakwe don samu jirgin farko.
To sai dai ce dan siyasar ya bar Otel din da ya zauna ne na Protea Hotel ba tare da sanarda yan sandar ba, wanda kuma a halin tsaro da ake ciki kwata-kwata bai dace a ce ya yi wannan kasassaɓar ba.
Sanarwar mai dauke da sanya hannun kakakin rundunar a Jihar Imo Mista Bala Elkana, ta ce kazalika kuma Gulak bai sanar da wasu jami’an tsaro cewa shi fa zai yi wannan tafiya ba.
To sai dai tuni Kwamishinan yan sandar Jihar Abutu Yaro ya bada umarnin gudanar da zuzzurfar bincike tare da ganin cewa an gano wadanda ke da hannu a wannan aika-aika.