Daga: Abbas Yakubu Yaura
‘Yan sandan jihar Kwara sun kubutar da wani dan kasar China da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi a ranar 3 ga watan Yuli a wani gini da ke kan titin Shao-Oloru.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Ajayi Okasanmi ya fitar a Ilorin ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/adamawa-sakataren-gwamnatin-tarayya-boss-mustapha-ya-yi-allah-wadai-da-harin-da-aka-kai-wa-iyalan-fasto/
Ya bayyana cewa jami’an ‘yan sandan da ke aikin ceto na nan a cikin daji domin kamo masu laifin.
Okasanmi ya kara da cewa, dan kasar Chinan da aka ceto a halin yanzu ana duba lafiyarsa domin sanin halin da yake ciki kafin haduwarsa da iyalansa.
“Matsalar da jami’an ceto suka yi wa masu garkuwa da mutane ya yi kamari, ta yadda masu laifin ba za su iya jurewa zafi ba, lamarin da ya sa suka yi watsi da wanda lamarin ya rutsa da su suka tsere don tsira da rayukansu.
“A wani labarin kuma, jami’an tsaro sun kama wasu mutane da ake zargin suna safarar sassan jikin mutane ne a lokacin da suke daukar kan mutum daga jihar Legas zuwa Ilorin.
“A bisa karfin bayanan da aka samu jami’an tsaro sun kama wani mutum mai shekaru 41 a Ilorin bisa aikata laifin.
“Wanda ake zargin a baya ya karbi kunshin ne daga wurin ajiye motoci. Bayan bincike ne aka gano wani kokon kan dan Adam da aka boye a cikin kwali da sunansa da lambar wayarsa a ciki.
“Binciken farko da aka yi a kan lamarin ya nuna cewa wanda ake zargin ya sayo kokon kan mutum, kan doki, kan biri da sauran kayayyaki.
“An gano sauran kayan a gidansa kuma ya amsa cewa yana da niyyar yin amfani da su wajen yin tsafi dan samun kudi,” in ji shi.
Okasanmi ya kara da cewa, kwamishinan ‘yan sanda, Mista Tuesday Assayomo, ya yabawa ‘yan sandan kan aikin da suka yi.
Ya kuma shawarci rundunar da ta gudanar da bincike da su tabbatar an cafke sauran wadanda ake zargi da yin garkuwa da su tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Ya kuma umarci kungiyoyin sufuri a jihar da su rika ba jami’an tsaro hadin kai a kowane lokaci wajen gudanar da babban aiki na kawar da miyagun laifuka, Okasanmi ya kuma bayyana.