‘Yan sanda a jihar Kogi sun ce sun ceto Farfesa John Alabi, Shugaban sashin Gudanarwa a Jami’ar Jihar Kogi, tare da wasu mutane uku daga hannun masu garkuwa da mutane.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, ASP William A. Aya neya tabbatar da wannan labarin a jiya Lahadi a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce Farfesa Alabi ya shaki iskar ‘yanci ne a daren ranar Asabar din da ta gabata, bayan kwanaki shida a hannun masu garkuwa da shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: El-Rufa’i ya nada Kwamitin Ziyara na jami’ar KASU
Ya Kuma kara da cewa, an sake sada shi da danginsa, duk da cewa ya bai ce komai ba, kan ko an biya kudin fansa ko a’a, don a sakin Farfesan.
A wani labarin Kuma na daban.
An samu barkewar cutar a kusa da yankin Ireti Ayo na Ilesa, yayin da aka gano wasu ma’aurata, Eso Olasunkanmi da Eso Fisayo sun mutu bayan sun ci a cikin abincin mai dauke da cutar.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadin data gabata, an gano ma’auratan ba su da rai a cikin dakin su.
Duk da haka an tattara cewa ma’auratan sun ci abincin daren Juma’a amma yanayin mutuwar su mai ban mamaki bai bayyana ba tukuna.
Wani mazaunin yankin, Wale Banjo, yace babu wanda ya san abin daya same su amma an gan su da farko a ranar Juma’a, 1 ga watan Oktoba saboda hutun da ake yi sai kawai ganin gawarwakinsu a kayi da yamma.
Opalola ya bayyana cewa an kai gawawwakin zuwa asibiti domin gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwarsu.
“An kai gawar ma’auratan asibiti domin a binciki gawar. Sakamakon zai iya taimaka mana mu gano sirrin dake bayan mutuwarsu.ya kara da cewa “A halin yanzu, ba zan iya bayyana abin da ya kashe su ba har sai bayan kammala binciken gawar.”