Daga: Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ceto mutane 12 da aka yi garkuwa da su, ciki har da wani jariri dan watanni biyar bayan wata daya da suka shafe a hannun masu garkuwa da su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Muhammad Shehu, wanda ya bayyana hakan a jiya, ya ce wadanda aka sace daga kauyen Rungawa da ke karamar hukumar Talata Mafara, an tsare su ne a sansanin wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Bello Maibille, da ke Dajin Kare-kukanka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Borno: Kotu Ta Bada Umarnin Sake Zaben Fidda Gwani Na PDP A Mazabar Hawul/Askira- Uba
Shehu ya ce an kubutar da su ne, a jiya Talata, a lokacin da jami’an ‘yan sanda da ke aiki da runduna ta 42 PMF Squadron Gusau, tare da hadin gwiwar ‘yan banga suka far wa sansanin.
Kakakin rundunar ya ce an kubutar da dukkan wadanda abin ya shafa ba tare da jin rauni ba.
Shehu ya kara da cewa an duba lafiyarsu ne a asibitin ‘yan sandan wayar tafi da gidanka ta 42 da ke Gusau, inda ‘yan sanda suka bayyana su tare da mika su ga iyalansu.
Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Kolo Yusuf, ya taya wadanda aka ceto ‘yancinsu murna, ya kuma ba su tabbacin cewa rundunar za ta kama wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Kolo ya yabawa jami’an kan kokarin da suke yi, ya kuma umurci dukkan ‘yan kasar da su kasance masu lura da tsaro tare da kai rahoton duk wani wanda ake tuhuma ga hukumar tsaro domin daukar matakin gaggawa.
A wani labarin kuma An Samu Gawarwakin Wasu Daliban Jami’ar KWASU 2 A Dakin Kwanan Dalibai
An samu gawarwakin wasu dalibai biyu na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU), Malete, Tobiloba Daniel da kuma masoyinta, Arewa Abayomi, a dakin kwanan dalibai na Daniel.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa wadanda suka mutun dukkansu dalibai ne masu matakin aji na 200 kuma suna tsaka rubuta jarabawa ne kafin faruwar lamarin.