Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce ta ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su, a kan hanyar Barde zuwa Keffi a karamar hukumar Kafanchan dake jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mohammed Jalige ne ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a Yau Alhamis a Kaduna.
Jalige ya ce, jami’an rundunar, lokacin da suka samu rahoton garkuwa da mutane sun bi diddigin ‘yan bindigar a cikin dajin.
Ya Kara da cewa, jami’an ‘yan sandan sun yi musayan wuta da Yan bindigan, Wanda hakan ya tilistamusu barin wadanda suka sace, Kuma suka tsere cikin daji da raunukan harsashi bindiga.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun hallaka mutane da dama, tare da Kona Gidaje a Zamfara
Ya Kuma kara da cewa, an yi nasarar kubutar da mutane shida daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba.
A cewarsa, an yiwa wadanda abin ya rutsa da su bayani sannan kuma an sada su da iyalan su.
Kazalika Jalige ya Kuma ce, “Ana ci gaba da kokarin ganin an kamo ‘yan bindigar da ke tserewa,” in ji shi.
A wani labarin Kuma makancin wannan.
An kashe fararen hula biyar lokacin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai farmaki a wani kauye da ke Arewa mai nisa a kasar Kamaru, in ji majiyoyi daga Hukumomin tsaron kasar.
Wasu gungun ‘yan ta’adda na Boko Haram dauke da muggan makamai a kan babura sun kai hari a kauyen Assigachia, da ke yankin Mayo Moskota a arewa mai nisa, kilomita kadan daga kan iyakar Nigeria, a cewar kwamandan yankin Janar Bouba Dobekreo.
Tun daga shekarar 2014, yankin kasar Kamaru ta tsakiyar Afirka, ta shiga yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram a cikin yankin na Arewa mai nisa.
Tawayen Boko Haram ya fara ne a tun a shekarar 2009 a Arewa maso gabashin Nigeria, kafin ya bazu zuwa kasashen makwabta. Tun daga wannan lokacin, sama da mutane 36,000 (galibi Yan Nigeria) aka kashe, kuma sama mutane miliyan 3 sun tsere daga gidajensu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Sai da a bangaren hukumomin kasar Kamaru kuwa, samar da kuɗi wurin yakar matsalar tsaro ya kasance babban ƙalubalen, wurin yaƙi da ‘yan ta’adda.