By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun ceto wani yaro mai shekara 17 da aka yi garkuwa dashi a dajin Sabon Birnin dake karamar hukumar Igabi a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Mohammed Jalige, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar ranar Lahadi a Kaduna.
Jalige yace, a ranar Asabar din data gabata, jami’an rundunar a lokacin da suke sintiri a dajin Sabon Birnin, sun jiyo karar harbe-harbe da ake yi a cikin dajin.
Ya ce jami’an sun yanke shawarar matsawa da karfi kusa da wurin domin gano abin da zai iya haddasa irin wannan abu.
“Jami’an ‘yan sandan sun kai farmaki ne a yankin da masu garkuwa da mutanen suke inda aka yi musayar wuta mai tsanani wanda ya yi sanadin kubutar da wani mai suna Sani Adamu mai shekaru 17, mazaunin tsohon filin jirgin saman Sabon Gida, yayin da ‘yan fashin suka tsere da raunuka daban-daban.
“Ba tare da bata lokaci ba aka kai wanda aka kubutar zuwa cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Kutungare domin kula da lafiyarsa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Bincike na farko ya nuna cewa an sace wanda lamarin ya shafa ne a lokacin da yake aiki a gonar shinkafa dake kusa da kauyen Afaka a karamar hukumar igabi a Kaduna,” a cewar sa.
Jalige yace ana ci gaba da kokarin ganin an ceto wasu da abin ya rutsa da su idan akwai su da kuma kawar da abubuwan da suka faru da su.
“Rundunar ‘yan sandan tana kira ga jama’a da kada su karaya da wadannan kebantattun al’amura kuma su kai rahoton duk wani harin sace-sacen da aka samu a yankunansu domin hukumar ta dauki matakin gaggawa.” Inji Jalige.