By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi, a ranar Juma’a, ta ce ta ceto sama da mata da maza 32, wadanda suke tsakanin shekaru 16 zuwa 17, daga hannun masu safarar mutane, wadanda ake zargin sun ajiye su a wani gida mai daki biyu, dake unguwar Okposi Umuaghara, a cikin unguwar Karamar Hukumar Ezza ta Arewa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP. Aliyu Garba, ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargi da fataucin tare da wadanda abin ya shafa a sashin B na rundunar ‘yan sanda a Abakaliki, dake babban birnin jihar.
Ya ce wadanda ake zargin sun yi safarar yaran ne daga sassa daban-daban na kasar domin yin aikin tilas da kuma lalata da su.
Sannan ya kuma kara da cewa an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ne biyo bayan batan wata karama yarinya, mai suna Nwankwo Ijioma wacce ta fito daga kauyen Uterufie da ke karamar hukumar Ebonyi ta jihar ta kai rahoto ga ‘yan sanda, inda ta bayyana cewa ‘yarta daya mai suna Mis Nwankwo Childera mai shekaru 14, waɗanda suka bar gidansu a watan Agustan shekarar 2021, ba a gan su ba.
Garba ya ce, “A dalilin bincike, an gano takardar tallar wani kamfani mai taken ‘NEO life’ mai dauke da lambar waya a dakin ‘yar. Inda aka gano mai wayar, wanda daga baya aka bayyana sunansa da Christian Nwankwo, ‘M’, mai shekaru 19, kuma an kama shi.
“An yi safarar yaran ne daga sassa daban-daban na kasar nan kuma ana amfani da su wajen yin aikin tilas da kuma lalata da su, da sunan kayayyakin kamfanin sadarwa na hawking NEO.
“Wadanda ake zargin sun yi hayar dakuna biyu (2) a dakin ajiyar kudi na Diamond Villa daura da sashin kula da lafiya na jami’ar jihar Ebonyi, harabar PRESCO, a matsayin wurin zama ga wadanda abin ya shafa.”
CP ya ci gaba da cewa an kama wani Nwagboduhu Ekene mai shekaru 20 da Nwaoko Godwin mai shekaru 24 da kuma wani daya tare da fataucin yara kanana 32 a maboyar su dake Okposi Umuaghara.
Kazalika ya kara da cewa yara 32 da aka yi safarar su sun fito ne daga jihohin Enugu, Ebonyi, Imo, Anambra, Akwa-Ibom, Cross River, Benue, Abia da jihar Ribas.