Daga: Abbas Yakubu Yaura
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Edo sun ceto mutane 33 da aka yi garkuwa da su, ciki har da wani yaro dan shekara uku, yayin da wasu biyar sukayi batan dabo, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito
An tattaro cewa wadanda iftila’in ya afkawa na tafiya ne daga Agbor zuwa Benin a lokacin da wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa da su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ma’aikatan Bogi: An Gano Wasu Da Ke Satar Kuɗaɗe Daga Jiha A Ƙaramar Hukuma ~ Sakataren Algon
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Chidi Nwanbuzor, ya ce ‘yan sandan sun samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun fito daga cikin daji a kan titin Agbor-Uronigbe-Obiaruku inda suka yi awon gaba da wata motar bas Toyota Hiace da ta taso daga Agbor zuwa Warri suka shiga cikin dajin da su.
Ya ce wadanda ke cikin motar ‘yan kungiyar kwallon kafa ta Itugbe Kings, Warri ne a jihar Delta.
“Rundunar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sojoji, ‘yan banga da kuma tawagar ‘yan sandan jihar Delta da ke kan iyakar jihar sun tattara tare da karade cikin dajin wanda ya yi sanadin kubutar da mutane 32 daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su a ranar 13 ga watan Agusta.
Ya ce yayin da ake bayyana wadanda abin ya shafa, an gano cewa har yanzu wasu biyar suna tare da masu garkuwa da mutanen, inda ya kara da cewa ana ci gaba da karade dajin domin ceto su.
Nwanbuzor ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga a wani harin sun kai hari kan wasu mutane biyu a cikin wata mota kirar Toyota Corolla da ta taso daga Bayelsa zuwa Agbor.
Ya ce duk da cewa sun tsere, daya daga cikin mutanen, Ibegu Daguapu, wanda aka harbe shi a kafadarsa ta dama, yana karbar magani a wani asibiti.