Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, sun ceto wasu ‘yan mata guda uku da aka yi yunkurin safararsu daga jihar Filato.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Zubairu Aminuddeen, shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a garin Dutse a ranar Laraba.
Aminuddeen y ace wadanda aka so safarar su din sun hada da Blessing Lawrence, mai shekara 20, sai Kindness Ezra, mai shekara 21, sai kuma Christiana Samuel, mai shekara 21 wanda yake duk mazauna Ray Field Mai Adiko ne dake jihar Filato.
Aminudeen ya ce an ceto ‘yan matan ne a ranar 26 ga watan Maris din 2021 a garin Babura dake karamar hukumar Babura a jihar.
Ya ci gaba da cewa; wani mutum ne mai suna Shu’aibu ya nemi ya yi safararsu zuwa kasashen waje ta jamhuriyyar Nijer daga Kano. Inda Shu’aibu yana hango ‘yan sanda ya jefar da su a daji ya ranta a na kare zuwa inda ba a tantance ba har yanzu.
‘Yan sandan sun ce ya yi yunkurin safarar matan ne zuwa kasar Tunisiya. Kamar yadda wani mai suna Chika ya yaudari ‘yan matan cewa za a kai su kasar ta Tunisiya ne domin su samu rayuwa mai kyau.
Kakakin ‘yan sandan ya ce tuni aka sada ‘yan matan da hukumar dakile safarar mutane wato NAPTIP reshen jihar Kano. Inda ya ce ‘yan sanda na ci gaba da binciken wadanda ake zargi domin cafko su.