Sashin rundunar yan sanda dake yaki da Yan kungiyar Asiri reshen jihar Delta, SACU, ya dakile wani yunkuri na kungiyar Asiri ta Black Ax a cikin garin Onicha-Ugbo na karamar hukumar Aniocha ta Arewa dake jihar.
Rundunar yan sandan ta kuma cafke mutane 10 da ake zargin yan kungiyar asiri ne, a cikin wani daji yayin da suke daf da fara tsubbace-tsubace.
Rahotanni na nuna cewa, an samu bindiga kirar gida guda daya, da harsasa masu kisa da tsayi 9mm, daga hannun wadanda ake zargi.
Rundunar yan sandan ta jihar Delta, karkashin jagorancin CP Ari Muhammed Ali, ya tabbatar da rahoton a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar wato, DSP Bright Edafe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 6 sun mutu a wani arangama tsakanin Jami’an Tsaro da Mabiya Shi’a
Sanarwar ta ce, “An kwato wasu gayyayyaki da ake kyautata zaton cewa Tabar Wiwi ce, mota kirar Honda daya da Mai dauke da lambar; Lagos KSF 586 DU, babura biyar, da dai saunaran su. ”inji shi.
DSP Edafe ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu da zaran an kammala gudanar da bincike.