By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja tace ta damke wasu mutane hudu tare da kwace motoci 21 bisa laifin yin tseren mota da aikata wasu laifuka makamantan su jiya a Abuja.
Jami’iar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja, DSP Josephine Adeh ce ta bayyana hakan a wata sanarwa data fitar ranar Litinin a Abuja. Adeh ta ce an kama wadanda ake zargin tare da tsare motocin a karkashin doka ta 228 na dokar hana zirga-zirgar motoci da sauran laifuka makamantansu.
Jami’in hulda da jama’a ta ce rundunar ‘yan sandan karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da babban birnin tarayya Abuja, Babaji Sunday, ta cafke tare da daure motocin a ranar Lahadi.
Tace an kama wadanda ake zargin ne a kusa da hanyar Muhammadu Buhari, a unguwar Inshora ta Nicon inda suka hadu da kasuwanci kamar yadda suka saba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja tun farko ta bayar da umarnin cikakken aiwatar da dokar hana duk wani nau’in wasa da suka hada mota da tseren gudu a yankin.
Wanda kwamishinan ya umurci dukkan jami’an ‘yan sanda na shiyya-shiyya da kwamandojin yankin su tabbatar da aiwatar da cikakken haramcin hana tseran mota yankin nasu.
Umurnin ya biyo bayan koken da jama’a suka yi kan barazanar rashin da’a, da kasadar rayuka, da barnatar da dukiyoyin jama’a da kuma muhimman ababen more rayuwa na kasa da tseren motar suka haddasa.