By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta kama wani mai garkuwa da mutane dan shekara 45, wanda ke haddasa rashin barci ga mazauna kananan hukumomin Akwanga da Wamba na jihar.
Wanda ake zargin Mohammed Igbira, an tura shi gidan yari da ke Jos, babban birnin jihar Filato saboda munanan ayyukansa, amma daga baya ya samu damar tserewa zuwa jihar Nasarawa inda ya rika addabar jama’a har aka sake kama shi.
A bincike da Jaridar Dimokuradiyya ta gudanar ya nuna cewa jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke sashin Wamba ne suka kama wanda ake zargin yana cikin kungiyar masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan fashi da makami.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu a garin Lafia, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel ya ce, “’Yan sanda sun samu labarin cewa wani da ake zargin dan kungiyar masu garkuwa da mutane ne da ‘yan fashi da makami da ke aiki a tsakanin karamar hukumar Akwanga da Wamba ta jihar Nasarawa an han geshi a babban birnin Wamba.
“Bayan samun labarin, jami’an ‘yan sandan da ke aiki a sashin Wamba sun hanzarta kai farmaki inda suka kama wanda ake zargin, mai shekaru 45 Mohammed Igbira.
Ya ci gaba da cewa, “Bincike da aka yi ya nuna cewa wanda ake zargin dan garkuwa ne da aka kama aka tura shi gidan yari a Jos, jihar Filato amma ya tsere daga hannun doka a lokacin da aka kai wa gidan yarin hari a ranar 30 ga watan Nuwambar shekarar 2021.
“Saboda haka, rundunar ‘yan sandan Najeriya da hukumar gidan gyaran hali a Jos, jihar Filato, sun zo ne domin gano wanda ake zargin, kuma rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta mika musu wanda ake zargin domin ci gaba da bincike.”
Sai dai PPRO ya ci gaba da cewa, Kwamishinan ‘yan sandan, Mista Adesina Soyemi ya zayyana jami’an hukumar zuwa gandun daji da garuruwa a fadin kananan hukumomin jihar 13 domin tabbatar da cewa muhallin ya kasance lafiya ga daukacin mazauna jihar.