By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da lalata na’urar taransifoma da sauran na’urorin lantarki a kauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar.
Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a Gusau ranar Alhamis, ta hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Muhammad Shehu.
Osinbajo Ya Isa Jihar Anambra, Domin Ganawa Da Masu Ruwa Da Tsaki Na Jam’iyyar APC
A cewar Malam Shehu, kamen ya biyo bayan kiran da aka samu daga Manajan kamfanin rarraba hasken wutar lantarki PHCN, reshen Tsafe, game da barnatar da na’urar taransifoma da sauran na’urorin lantarki da aka yi a kauyen Wanzamai.
Ya bayyana cewa an cire adadi mai yawa na waya conductor na aluminium wanda kudinsa ya kai kusan Naira 800,000.
Kakakin ‘yan sandan ya ce wadanda ake zargin sun fito ne daga kauyen Wanzamai.
“Jami’in dan sandan shiyyar Tsafe, ya yi aiki da bayanin daya samu, inda ya kama wadanda ake zargin da narkakkar waya mai dumbin yawa.
“A yayin da ake yi masa tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa, kuma sun kara ambato wasu abokan huldar su da aikata laifuka, wadanda a yanzu haka suke hannunsu.
“Rundunar, karkashin jagorancin CP Ayuba Elkanah, tana amfani da dabaru daban-daban don kama wadanda ake zargi da gudu tare da gurfanar da su a gaban kotu,” in ji Mista Shehu.
Ya kuma bai wa mazauna jihar tabbacin hukumar na ba da cikakkiyar kariya ga cibiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu a fadin jihar, ya kuma shawarce su da su kiyaye tare da bayar da rahoton duk wani yunkuri na lalata duk wani abu na jama’a, domin daukar matakin gaggawa.
NAN
Comments 1