By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wani Fasto mai kula da cocin Spirit-filled International Christian, Olomore Abeokuta dake jihar Ogun, Fasto Timothy Oluwatimilehin da laifin yaudarar wata uwar gida da ‘ya’yanta mata guda biyu wajen rabata da iyalinta tare da ajiye su a gidansa.
Faston, bayan haka ya fara kwana da kowanne daga cikin su akai-akai.
Mijin matar wanda ya kasa kubutar da matarsa da ‘ya’yansa mata guda biyu daga hannun Fasto Oluwatimehin kan wasu shakuwa da suka shafi soyayya, ya garzaya ofishin ‘yan sanda na Adatan inda ya kai rahoton yadda wanda ake zargin ya ware matarsa da ‘ya’yansa mata, ya kama su kuma ya kula da su. akai-akai cin zarafin jima’i kan su ukun.
Jami’an ma’aikatar harkokin mata ta jihar Ogun ne suka taimaka wa mijin daya rasa ransa inda ya kai rahoto ga ‘yan sanda abin da ya faru da shi, inda suka yi kaca-kaca da wannan aika-aika.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya.
Oyeyemi, mataimakin Sufurtandan ‘yan sanda (DSP) ya ce jami’in ‘yan sanda na sashen (DPO) reshen Adatan, Sufeto Abiodun Salau, ya tura jami’an binciken wadanda suka damko Fasto.
Kakakin ‘yan sandan ya ce wanda ake zargin ya amince cewa ya aikata laifin da ake zarginsa da shi.
“Faston ya amsa laifin aikata laifin amma ya roki gafara. A cikin ikirari nasa, ya bayyana cewa ya yi amfani da wata ‘yar rashin fahimta da aka samu tsakanin matar da mijinta wajen aiwatar da wannan aika aika.
“Kwamishanan ‘yan sanda, CP Lanre Bankole ya umurci sashin yaki da fataucin bil’adama da yi wa yara aiki na sashen binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar da su karbe lamarin tare da yin bincike mai zurfi da nufin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da wuri .”