Wani matashi a birnin Ilori na Jihar Kwara ya kada kararrawar cewa yan sanda sun yi ram da wasu masu kunnen ƙashi kan haramcin da gwamnatin tarayya ta yi.
Da ma dai a ranar Juma’a ne gwamnatin tarayyar ta bada umarnin haramta ayyukan shafin na tuwita a fadin kasa baki ɗaya.
To sai dai duk da wannan umarni da kuma jan kunne da gwamnatin ta yi, bai hana wasu daga cikin yan kasa bi ta barauniyar hanya duna amfani da tuwitar ba.
Wata kila bisa ganin wannan taurin kai ne ya sa jami’an yan sanda suka bazama gari a birnin Ilori inda suka fara aikinsu kamar yadda da ma tun farko aka bayyana cewa za a yi.
Matashin da ya bayyana wannan labari duk da cewa bai ayyana sunansa ba, ya ce jami’an yan sanda sun kutsa unguwar Tanke Oke Odo dake birnin na Ilori inda bayan duba wayoyin abokan nasa ne, suka tabbatar da cewa akwai manhajar tuwita din, nan take suka cika hannu da su.
Idan ba a manta ba, a ranar Asabar Antoni Janar na kasa kuma ministan Shari’a Abubakar Malami, ya bada umarnin kama duk wani mai kunnen kashi da ya ci gaba da Amfani da kafar ta tuwita bayan da gwamnatin tarayya ta haramta amfani da shi.