Rundunar yan sandan jihar Enugu ta karkame ofishin jam’iya Mai Mulki na APC dake garin Enugu, domin tabbatar da zaman lafiya, da kuma bin doka da oda a Jam’iyar dama jihar baki daya.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, an hana wasu Shuwagabannin jami’iyar da kuma wasu jiga-jigan ta, shiga Babban Ofishin jam’iyar na Enugu ne, biyo bayan wani rikicin da ya balle kan shugabanci.
Hakan na zuwane bayan kada kuri’ar yanke kauna da ya yi sanadiyar tumbuke Shugaban jam’iyar a jihar wato Dakta Ben Nwoye a kan mukamin shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matsalar Tsaro: Gwamnatin Kaduna ta bukaci Karin Jami’an soji
Kamfanin Dillancin Labaran Nigeria NAN ya ruwaito cewa, wasu mambobin jam’iyar 42 na kwamitin gudanar war jam’iyar a Enugu ne, su ka kada wandannan kuri’u a jiya laraba.
Shugaban kwamitin ya bayyana wa manema labarai cewa, sun dauki wananan matakin ne, bayan Shugaban jam’iyar a jihar ya yi Fatali da kundun tsarin gudanar war jam’iyar.
A wani labarin Kuma na daban.
A jiya Laraba ce dai, hukumomin Babban Birnin Tarayya Abuja, su ka rushe gine-gine akalla guda 2,000 da a ka yi su ba bisa ka’ida ba, a yankin Mpape.
Shugaban kwamitin tsabtace Birnin Ikharo Attah ya ce, an dauki matakin ne, domin tsabtace yankin baki daya.
Ya kara da cewa, Mazauna yankin ne, da kuma dillalan gidajen haya, su ka bukaci Ma’aikatar da ta rushe gine-ginan, inda ya ce, gine-ginan anyisu ne ba bisa ka’ida ba Kuma a gefen hanya, wanda yanzu rushewar ta samar da wal-walar al’uma, da kuma na ababen hawa.
Ya ce, ” Al’umar yankin na Mpape ne su ka bukaci Ministan Abuja Muhammad Bello da rushe wasu a gine-gine, domin tsabtace bakin hanya” inji shi.
“Mun kuma basu isasshen lokacin su ta shi, amma wasu daga cikin su na tunanin cewa, babu wanda ya Isa ya tsabtace Mpape” a cewar shi.
Lokacin da ya ke jawabi, Peter Olumoji jami’in a hukumar tsaro ta farin Kaya DSS ya ce, Mafi yawaicin gine-ginan da aka rushe anyi su ne ba bisa ka’ida ba, Kuma bata gari ne su ka mamaye su.
Olumuji ya Kara da cewa, a lokuta da dama an sha samun rahotannin ta’addanci na karuwa a yankin Mpape, sabida maboya da masu gidajen haya suka ba su a yankin.
Sai dai a na su bangaren, Mazauna yankin da lamarin ya shafa, sun koka kan karancin lokaci da ba su samu ba a wurin hukumomin Birnin, kafin rushe gine-ginan.