Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa jami’anta sun kashe wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne guda biyu tare da kwato bindiga kirar AK-47 da babur a ranar Asabar a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Mohammed Jalige, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Kaduna.
Jalige ya ruwaito cewa, farmakin da jami’an tsaor suka ci gaba da yi ya haifar da sakamako mai kyau inda aka samu nasarar kashe ‘yan bindiga biyu, tare da kwato bindiga kirar AK-47 da kuma babur guda daya.
Ya bayyana cewa an samu rahoton ta hannun DPO Kidandan a ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe 08:00 na safe cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu manoma da ba a tantance adadinsu ba da ke aiki a gonakinsu a kauyen Timburku da ke unguwar Galadimawa a karamar hukumar Giwa.
A cewarsa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Yekini Ayoku, ya ba da umarnin kai rundunar ‘yan sandan mash kwantar da tarzoma da ke kusa wato Operation Restore Peace da kuma mai suna Operation Puff Adder II zuwa yankin.
Ya ce, “A cikin zazzafar huldar da ta faru da ‘yan bindigar, kwararrun tawagar ‘yan sanda sun yi galaba da karfinsu.”
Jalige ya ce hakan ne ya sa aka kashe biyu daga cikin ‘yan bindigar, inda aka kwato bindigu kirar AK-47 guda daya dauke da alburusai guda biyu, babur daya da kuma adduna, yayin da aka ceto wadanda abin ya shafa (manoma) ba tare da wani rauni ba.
Ya ce, “Yana da kyau a sake nanata cewa ba za a iya cimma wannan nasarar ba idan ba tare da rahoton da ya dace da ‘yan kasar ba ya kamata su dun ga bai wa jami’an tsaro ba.
“Kwamishanan ‘yan sandan, ya sake yin kira ga jama’a da su rika baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sirri da su gaggauta kai rahoton duk wani yanayi na damuwa, domin ya ba su tabbacin daukar matakin da ya dace.”
Jalige ya ci gaba da cewa, tuni aka fara gudanar da bincike kan lamarin yayin da ake ci gaba da sa ido da kuma sintiri domin dakile duk wani abu da ya faru saboda an dawo da zaman lafiya a yankin da lamarin ya shafa.
Kakakin, ya kuma bukaci jama’a da su bayar da bayanai kan duk wani mutum ko kungiyar da aka samu raunukan harsashin bindiga a jikin su.